Ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ya mika ma’aikatar tsaro ga babban sakatare, Dr. Ibrahim Abubakar Kana a daidai lokacin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta cika shekaru takwas.
Takaitaccen bukin mikawa da karbar ragamar aiki da aka gudanar a hedkwatar ma’aikatar tsaro da ke Abuja kuma ya samu halartan ma’aikatan gudanarwa da na sojoji da na fararen hula.
Takardun da ke kunshe da cikakkun bayanai na tafiyar da Janar Magashi tun daga ranar da ya karbi ragamar shugabancin ma’aikatar an rattaba hannu a kai a hukumance aka mika shi ga shugaban gudanarwa, babban sakatare domin ya karbi ragamar aiki kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarta.
Janar Magashi, wanda a karkashinsa Sakatarorin dindindin hudu suka yi aiki a jere ya yaba da goyon bayan Babban Sakatare, Dokta Ibrahim Abubakar, da daraktoci, da ma’aikata da kuma taimakon Ministoci saboda muhimmiyar rawar da suke takawa wajen ganin ya samu nasarori a cikin shekaru hudu da suka gabata a ofis.
Ya kuma yaba da goyon bayan da babban kwamandan, shugaban kasa Muhammadu Buhari, da hadin kan hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor da hafsoshin sojan kasar suka ba shi, bisa sadaukarwar da suke yi na kishin kasa wajen kare martabar kasa a karkashin sa.
Ministan ya kuma yabawa shugabannin cibiyoyi da hukumomin soji da ke karkashin ma’aikatar bisa biyayyarsu da yi wa kasa hidima.
Ya bayyana cewa tafiyarsa ta hidima a matsayinsa na mai girma ministan tsaro ya bada gadon bin diddigi da sanin ya kamata wajen tafiyar da kudaden jama’a tare da tabbatar da daidaito tsakanin ma’aikatu tare da inganta karfin sojojin fada, gyare-gyare daban-daban ingantattu, jin dadin ma’aikata, horo da sauransu.
Babban Sakatare, Dr. Ibrahim Kana ya taya Ministan murnar samun nasarar kammala rangadin aiki, inda ya mayar da ma’aikatar tare da barin ta fiye da yadda ya hadu da ita shekaru hudu da suka gabata.
Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (rtd) ya karbi ragamar kula da ma’aikatar tsaro da aka kafa a shekarar 1958 a matsayin babban jami’inta na 24 a ranar 21 ga Agusta 2019 a farkon wa’adi na biyu na shekara takwas na Kwamandan Shugaban Rundunar Sojin Najeriya, Muhammadu Buhari.
Leave a Reply