Mayu 29: Gwamnan Jihar Neja Ya Sallami Wasu Masu Bashi Gabanin Mika Mulki Ga Sabuwar Gwamnati.
Nura Muhammad
Gwamnan jahar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya Abubakar Sani Bello ya sauke wasu daga cikin masu rike da mukaman siyasa gabanin mika mulki ga Sabuwar Gwamnati.
Sanarwar hakan na kunshe ne cikin takardan da sakataran gwamnatin jahar Ahmed Ibrahim Matane ya fitar aka rabawa manema labarai a garin Minna fadar gwamnatin jahar.
A cewar sakataran gwamnatin wadanda sallamar ta shafa sun hada da Shugabanin board na hukumomin gwamnati, sai kodinatoci na shirye shirye da manyan masu baiwa gwamna shawara, da masu taimakwa gwamna kan harkokin siyasa da sauran mukaman siyasa.
A cewar sanarwar kwamishinoni zasu kasance kan mukamin su har izuwa ranar 29 ga watan na mayu da za’a Mika mulki ga sabuwar gwamnati.
Ahmed Matane ya ce akwai babban daraktan hukumar bada lamunin kudi ga kananan yan kasuwa, da na hukumar dake kula da tabkin Gurara da sauran ma’aikatun da wa’adin mulkin su ya kawo karshe.
Sakataran gwamnatin ya Kara da cewar an Kuma umurce dukkanin wadanda sallamar ta shafa da su Mika ragamar jagoranci ga sakatare Mai kula da harkokin siyasa a ofishin sakataran gwamnati kafin ranar 29 ga watan na mayu.
A cewar Ahmed Ibrahim Matane gwamna jahar Abubakar Sani Bello ya Yaba da yadda suka bada gudumuwar su don ganin jahar ta cigaba, ya Kuma Yi musu fatan alheri.
Leave a Reply