Take a fresh look at your lifestyle.

FADAR SHUGABAN KASA TA TABBATAR DA TSARO GA ‘YAN NAJERIYA

0 279

Mataimaki na musamman akan harkokin ‘yan Jarida ,Garba Shehu yace fadar shugaban kasa ta tabbatar wa al’umar Najeriya cewa tana kokari akan shawo kan kalubalen tsaron da kasar ke fama da shi.

Garba Shehu ya kuma yi kira  ga wadanda ke yada labaran karya da zasu iya tada hankalin Jama’a da su shiga tai tayin su.

 “Parpaganda da ‘yan Taadda ke anfani da suke anfani das u wajen tayar wa al’uma hankali na tirsasa wa gwamnati amincewa da bukatun siyasar su , ba wani sabon abu ba a duk fadin duniya.

“Kada a tsamanin Jamian tsaro basu san abunda ke faruwa ba.Suna da nasu shiri da hanyoyin da  suka dace wadanda ba sai bsun anar a kafafen yada labarai ba.”

Mataimakin Shugaban kasar yace rundunar soji ba zata sanar da irin rawar da zata taka na dabarun shawo kan lamarin ba akan yunkurin tan a ceto duk wadanda akayi garkuwa da su.

 “Halin da mutanen da aka kama a Jirgin kasa da ‘yan taadda sukayi,sai anyi taka tsantsan: matakan rowan bama bamai a yankin da suke kamar yadda al’uma ke kira zai iya tada hankalin jama’a,a to su kuma wadanda akayi garkuwa da su fa? Basu aikata wani laifi ba,Jirgin kasa kurum suka hau.

“Bai kamata ace jami’an tsaro ba su maida hankali akan aikin su ba. Suna gudanar da aiyyukan su a matsayin sun a kwararru,saboda haka ya kamata al’uma su basu gudummowar da suke bukata,” inji shi.

Ya kara da cewa ba a san Najeriya da harkar Taaddanci abunda ake bukata shine hadin kai.

“’Yan Jarida ne keda alhakin taimaka wa halin da kasar ke ciki,tare da goyon bayan sun a yaki da abun da bata gari ke anfani da shi ta yanar gizo’’.

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *