Take a fresh look at your lifestyle.

Hukuma Ta Kai Ziyara Wuraren Da Zasu Fusnaci Ambaliya Ta Gargadi Mazauna Game Da Hatsarin Dake Gaba

0 119

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kaduna, KADSEMA, ta ziyarci wuraren da ake fama da ambaliyar ruwa a jihar, inda ta gargadi mazauna jihar kan hatsarin da ke tafe.

 

Mista Muhammed Mukaddas, Sakataren zartarwa na KADSEMA, ya ce sun kai ziyarar ne domin wayar da kan jama’a da kuma jawo hankalinsu ga hasashen NIMET.

 

NIMET ta yi hasashen cewa lokacin damina na shekarun zai yi nauyi fiye da shekarun baya kuma zai iya haifar da mummunar ambaliya.

 

Mukaddas ya ce galibin yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa a jihar ba su da aminci da zama a ciki, kuma kwamitin riko na jihar na kokarin ganin an kwato yankunan domin ceton rayuka da dukiyoyi.

 

Ya kara da cewa hukumar ta fara gudanar da ayyukan sa ido na yau da kullun a kananan hukumomin Sanga, Kaura Jamaa, Jaba da Kagarko (LGAs).

 

“Gwamnatin jihar ta fara aikin hakar koguna kafin damina domin rage yiwuwar samun ambaliyar ruwa, mun kuma wayar da kan jama’a kan bukatar su dauki nauyin kawar da gurbataccen ruwa tare da kaucewa zubar da shara a hanyoyin ruwa.

 

Sakatariyar zartaswar ta ce hukumar za ta tabbatar da cewa mutanen da ke zaune a wuraren da ake fama da ambaliyar ruwa sun koma wuraren dake kan tudu. “Mun shawarce su da su kasance cikin shiri su bar wuraren idan ruwan sama ya yi yawa,” in ji Mukaddas.

 

Ya ce sun lura da mutanen da ke rayuwa a hanyoyin ruwa, sun rubuta su, sannan kuma sun fara rusa wasu gidajen, tare da hadin gwiwar hukumomin da abin ya shafa a jihar.

 

Shi ma da yake jawabi, Mista Zakariya Solomon, ma’aikacin Hukumar Kula da Tsare-Tsare da Cigaban Birane ta Jihar Kaduna (KASUPDA), ya ce suna aiki tukuru tare da masu ruwa da tsaki domin rage tasirin ambaliya a cikin al’umma.

 

Ya bayyana cewa ana kokarin tsugunar da mutane a wasu yankunan da ake fama da ambaliyar ruwa akai-akai zuwa wasu wurare.

 

“Za mu isa gare su daidaiku kuma mu ga ko suna da takaddun da gwamnati za ta yi amfani da su wajen biyan su diyya,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *