Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC

0 88

Shugaba Bola Tinubu na cikin wata ganawa da gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC.

 

Taron wanda aka fara da karfe 10:00 agogon GMT, gwamnoni 19 ne suka halarta.

 

Wannan dai shi ne karon farko da shugaban ke ganawa da gwamnonin tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

 

A ranar Talatar da ta gabata ya gana da gwamnan babban bankin kasa da kuma babban jami’in gudanarwa na kamfanin man fetur na Najeriya.

 

A ranar Alhamis, ya gana da shugabannin tsaro, inda ya nemi hadin kan dukkan hukumomin tsaro, domin shawo kan kalubalen tsaro.

 

Ana sa ran samun cikakken bayani kan ganawar da shugaban kasa zai yi da Gwamnonin APC nan gaba.

 

Ana sa ran nan gaba zai gana da Gwamnonin Jihohi 36 na Tarayyar.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *