Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Najeriya Ya Nada Shugaban Ma’aikata Da Sakataren Gwamnati

0 155

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana nadin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shi, da Ibrahim Hassan Hadejia, tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata.

 

A ganawar da yayi da Progressive Governors Forum (PGF), shugaban ya kuma nada tsohon gwamnan jihar Benue kuma tsohon ministan ayyuka na musamman, George Akume, sakataren gwamnatin tarayya (SGF).

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na fadar gwamnatin jihar, Abiodun Oladunjoye ya fitar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *