Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tashi daga Najeriya ranar Talata 26 ga watan Yuli,2022 zuwa Laberiya domin halartar bukin samun ‘yancin kai a Laberiya.
Wannan tafiyar nada muhimmanci akan harkar tsaro da rayuwar Laberiya da sauran kasashen Yammacin Afirka.
A yau ne kasar Laberiya ke bukin samun ‘yancin kai daga ‘yan mulkin mallaka na shekara 175 da samun ‘yanci wanda itace kasar da tafi kowace kasar Afirka tsawon shekarun samun ‘yanci.
Ana sa ran a bukin Shugaba Buhari a matsayin shin a babban bako a wajen bukin zai gabatar da bayanai.
A sakon sako,mai Magana da yawun fadar shugaban kasa, Garba Shehu yace; “Wannan tafiyar zuwa Laberiya nada muhimmanci a dai-dai lokacin da ake samun rashin dai-daiton siyasa da hana juyin mulki shekaru da suka gabata bayan komawa ga tsarin Demokuradiya a yammacin Afirka.
“Laberiya, Saliyo da Najeriya na kan gabar gudanar da zabuka a shekara ta 2023 kuma ana sa ran Shugaba Buhari zai maida hgankali akan zabuka masu inganci da zaman lafiya.
Ya nuna muhimmancin zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka yana cewa; “Muddin baa laakari da bin doka da oda da tsarin mulkin kasa,ba za’a samu kwanciyar hankali da tsaro a ci gaba ba.
LADAN NASIDI
Leave a Reply