Shugaba Bola Tinubu ya aike da sakon ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Jamhuriyar Indiya kan hadarin jirgin kasa da ya yi sanadiyar mutuwar fasinjoji sama da 280 a kasar.
Mummunan hatsarin da ya rutsa da jiragen kasa guda biyu na fasinja da wani jirgin kaya a birnin Balasore na kasar Indiya, a jihar Odisha da ke gabashin kasar, ya afku ne a ranar Juma’a.
Baya ga wadanda suka mutu, wasu sama da 900 sun jikkata a wani hatsarin jirgin kasa mafi muni a tarihin baya-bayan nan.
A wata sanarwa da shugaba Tinubu ya fitar, ya bayyana hatsarin jirgin a matsayin mai tayar da hankali, yayin da yake jajantawa gwamnatin Indiya da iyalan wadanda abin ya shafa.
“Zuciya ta tana ga iyalan wadanda abin ya shafa a hatsarin jirgin kasa mai ban tausayi a jihar Odisha ta Indiya.
“Muna muamala da Indiya cikin ‘yan uwantaka a wannan mawuyacin lokaci. Hadari da alkaluman wadanda suka mutu ya yi yawa,saboda haka ya bukaci kasashen duniya su tallafa wa Indiya domin daukar matakin da ya dace kan wannan mummunan hatsarin.
“Ina mika sakon ta’aziyyata ga Mai Girma Firayim Minista Narendra Modi, da mutanen Indiya da iyalan wadanda suka hadarin ya shafa,” in ji shugaban.
Leave a Reply