Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Borno Ya Halarci Sallar Jana’izar Marigayi SSG Na Rana Na Uku

0 284

Gwamna Zulum na jihar Borno ya halarci sallar jana’izar marigayi sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Shuwa na kwana 3 a gidansa da ke kan titin Gambole a Maiduguri.

Zulum ya bayyana marigayi SSG a matsayin babban ma’aikacin gwamnati wanda ya kawo gyara a lokacin hidimarsa.

Ya ce, “Hakika babban rashi ne ga al’ummar Borno da Najeriya baki daya, Usman Shuwa, ya yi aiki a matsayin SSG na jihar Borno tsawon shekaru 8.”

“A lokacin da yake hidima ya yi kyau sosai, ma’aikaci ne mai jajircewa kuma mai kwazo, ya kawo sauye-sauye ga ma’aikatan gwamnati, musamman yadda ake tantance ma’aikatu da kuma bin doka da oda da sauransu, ina rokon Allah Ya saka masa da alheri Ya bashi zaman lafiya na har abada”.

“Ba shakka mutanen Borno za su tuna da shi saboda gudunmawar da ya bayar”.

Hakazalika, Zulum ya halarci Sallar Jana’izar Marigayi Hajjiya Mallam yar jam’iyyar APC, wacce ta rasu tana da shekaru 47 a duniya, Zulum ya isa gidanta dake Lawan Bukar tare da Sanata Ali Ndume, Sanata Kaka Shehu Lawan da dai sauransu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *