Shugaba Bola Tinubu, ya rantsar da George Akume a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarayya (SGF) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Takaitaccen taron wanda ya tara manyan baki da suka hada da wasu masu rike da madafun iko da tsaffin Gwamnoni, ya ga Akume ya yi rantsuwa da rantsuwar aiki da misalin karfe 11:06 na safe a cikin zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa.
Karanta Haka: Shugaban Najeriya Ya Nada Shugaban Ma’aikata, Sakataren Gwamnati
Cikin wadanda suka halarci bikin akwai mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima; Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan; Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara, shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr FolasadeYemi-Esan da matar sabon SGF, Misis Regina Akume.
https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1666371956084469761?ref_src=twsrc%5Etfw%7Ctwcamp%5Etweetembed%7Ctwterm%5E1666371956084469761%7Ctwgr%5E124ba7f8a77801cdd191f57372acf9259342c528%7Ctwcon%5Es1_&ref_url=https%3A%2F%2Fvon.gov.ng%2Fpresident-tinubu-swears-in-akume-as-secretary-to-government%2F
Leave a Reply