Take a fresh look at your lifestyle.

Sabuntawa: Sarakunan Gargajiya Sun Goyi Bayan Shugaba Tinubu

0 128

Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi-Ojaja II, ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya yi amfani da sarakunan gargajiya, kasancewar su na kusa da jama’a, wajen magance matsalar rashin tsaro da ke addabar wasu sassan kasar nan.

 

 

Ya ba da shawarar ne a ranar Juma’a, yayin ziyarar ban girma da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Najeriya (NCTRN) ta kai wa Shugaban kasa a Cibiyar Taro na Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

 

 

Karanta Haka: Shugaba Bola Tinubu Ya Gana Da Sarakunan Gargajiya

 

 

Ooni, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban sarakunan Najeriya, ya ce:

 

 

“Akwai wuraren da muke son yin aiki tare da ku, daya daga cikinsu shi ne tsaro. Lokaci ya yi da za a ƙara amfani da mu, ba muna cewa muna zaman banza ba amma don sauƙaƙe aikinku, ku yi amfani da mu.

 

 

“ Tushen kasar nan a yau shi ne sarakunan gargajiya. Mun zo nan don yin alkawarin aminci da goyon bayanmu. Muna son yin aiki tare da ku don tabbatar da barin gado. Kada ku raina abin da sarakunan gargajiya za su iya yi,” inji shi.

 

 

Tun da farko, Sarkin Musulmi kuma shugaban NCTRN Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ce ziyarar al’ada ce ta sarakunan gargajiya a duk lokacin da aka samu sauyi a shugabancin kasar.

 

 

Ya ce sarakunan mutane ne masu sana’o’i daban-daban tun daga aikin soja zuwa bangaren shari’a da kuma ‘yan kasuwa, wadanda suke da abin da ya kamata su ba da tasu gudunmawar don ci gaban al’umma, yana mai cewa, “duk lokacin da kuka kai mu nan za mu zo.

 

 

Sarkin Musulmin ya ce sarakunan ba sa kishin Shugaba Tinubu a wannan lokaci da dimbin kalubalen da kasar ke fuskanta amma ya nuna kwarin guiwar cewa tare da hadin kan sa da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima za su kai ga nasara.

 

 

Ya ce: “Mun gode wa Allah da yadda aka gudanar da zaben cikin sauki. Mutane da yawa marasa kyau sun yi tunanin kasar nan za ta rushe amma har yanzu muna nan. Muna nan don ku, ga jama’armu da kuma kasarmu. Idan ba ku tuntube mu ba, za mu tuntube ku. Muna yi muku fatan alheri cikin koshin lafiya.”

 

 

Haka kuma sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.

 

 

Taron wanda aka ce yana cikin tuntubar da shugaba Tinubu yake yi da masu ruwa da tsaki a fadin kasar, ana sa ran za a tattauna batutuwa daban-daban da suka hada da yadda za a samu waraka a kasa da hadin kan kasar.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *