Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya, DSS, ta tabbatar da cewa hukumar ta DSS ta kama tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
A wata sanarwar Jami’in hulda da jama’a na DSS (PRO), Peter Afunanya, ya tabbatar da hakan.
“Hukumar DSS a nan ta tabbatar da cewa Mista Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) na hannun ta saboda wasu dalilai na bincike,” in ji sanarwar.
Mai magana da yawun hukumar leken asiri ya bukaci jama’a musamman kafafen yada labarai da su yi taka-tsan-tsan a cikin rahotanni da labaran da suka shafi tambayoyin Mista Emefiele.
Sanarwar ta zo ne sa’o’i bayan hukumar DSS ta musanta ikirarin da ake yi na cewa Emefiele na hannun ta.
An yada rahotannin kama Emefiele a yanar gizo, bayan dakatarwar da aka yi a ranar Juma’a da yamma.
Tun da farko kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya ya musanta kama tsohon shugaban na CBN.
A wata sanarwa da ya fitar, “A halin yanzu, Emefiele ba ya tare da DSS,” in ji kakakin
Idan za a iya tunawa, Daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya sanar da dakatar da Emefiele.
“Shugaba Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin kasa, Mista Godwin Emefiele, CFR daga aiki ba tare da bata lokaci ba. Wannan wani ci gaba ne ga binciken da ake yi a ofishinsa da kuma sauye-sauyen da aka tsara a fannin hada-hadar kudi na tattalin arzikin kasar,” in ji sanarwar.
An umurce shi da ya mika al’amuran ofishinsa ga Mataimakin Gwamna (Ayyuka) Folashodun Shonubi, wanda zai yi aiki a matsayin Gwamnan Babban Bankin kasar har sai an kammala bincike da gyara.
Leave a Reply