Take a fresh look at your lifestyle.

Barista Abdulmalik Sarkin Daji Ya Zama Kakakin Majalisar Dokoki Jihar Neja Ta 10.

Nura Muhammad

0 179

Majalisar dokokin jahar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta zabe Barista Abdulmalik Sarkin Daji da ke wakilta Mariga a matsayin kakakin majalisar na 10.

Sabon kakakin majalisar wanda tsohon Shugaban karamar hukumar Mariga kana tsohon kwamishinan kananan hokumomi da masarautu na jahar Neja ya sami zama jagoran majalisar ne bayan da Dan majalisa mai wakiltar Bidda 2 ya gabatar da shi Kuma hakan ya sami amincewar sauran yan majalisun.

Saboda kakakin majalisar wanda akawun majalisa Alhaji Abdullahi Kagara ya gabatar bayan shan rantsuwa ya kuma sha alwashin yin aiki tukuru domin ganin jahar ta sami cigaba mai daurewa.

Barista Abdulmalik Sarkin Daji ya Kara da cewar majalisar zata yi duk mai yuwa wajan ganin sun yi aiki kafada da kafada da bangaran zartarwa domin kawo karashen matsalar tsaro da jahar ke fama da shi.

Kakakin majalisar ya kuma ce “bayan kasancewar na kakakin majalisar na sa an aikewa dukkanin manyan jami’an tsaro dake jahar takardan gayyata domin su zo su bada bahasi kan inda aka kwana a kokarin su na kawo karashen matsalar tsaro a jahar Neja don sanin hanyoyi da majalisar zata taimaka.”

Abdulmalik Sarkin Daji ya Kara da cewar ta hanyar sanin matsalolin su ne majalisar zata San inda Yakamata a bi wajan ganin an warware matsalolin ta yadda alumma zasu koma gidajan su domin cigaba da yyukan su na noma kamar yadda aka sansu da shi.

Har ila yau kakakin majalisar ya kuma bayana kudirin majalisar na baiwa bangaran zartarwar hadin kan da Yakamata domin tallafawa alummar jahar ta fannoni daban daban da zai taba rayuwar su

A jawabin sa Gwamnan jahar Neja Umar Muhammad Bago wanda mataimakin sa Comrade Yakubu Garba ya wakilta ya bayana kudirin gwamnatin sa na aiki da majalisar domin ciyar da jahar gaba.

Har ila yau Gwamnan ya kuma tunasar da yan majalisar irin kalubalen dake gaban su musamman yadda suka sha alwashin gudanar da ayyukan su bisa yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar masu.

Bayaga kakakin majalisar, majalisar ta kuma zabe mataimakiyar kakakin majalisa mace Afiniki Dauda dake wakiltan Gurara., Inda kuma tuni suka sha rantsuwar kama aiki.

Yanzun haka Yan majalisar jahar Neja 25 cikin 27 da ake da su ke zama sabbin zuwa ayayin da 2 suka sami damar komawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *