Take a fresh look at your lifestyle.

Kungiya Ta Baiwa Yara Sama Da Dari Uku Tallafin Karatu A Jihar Neja.

By: Nura Muhammad

0 327

Wata kungiya Mai suna Stella Maris Educational Foundation (SMEF) ta baiwa yara sama da dari uku wadanda iyayen su suka rasu da ma wadanda ke fama da cuta Mai karya garkuwar Jiki sakamakon cutar HIV/AIDS tallafin karatu a Minna, fadar gwamnatin jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya.

Da yake jawabi a lokacin da yake rabawa yaran kyaututtuka, wanda ya hassasa kungiyar Reverend Father Chiedozie Ezeribe ya ce kungiyar wace aka kafata a shekarar 2011 ta hada hannu da makarantu da dama a kauyuka domin baiwa yara tallafin karatu.

Rev Father Chiedozie ya Kara da cewar yanzun haka sama da yara dari da sittin ne suka anfana da kashin farko na tallafin da kungiyar ke badawa a duk wata.

A cewar sa “Muna da yara 164 wadanda iyayen su suka kamu da cutar Mai karya garkuwa jiki inda wasunsu ma sun mutu, bamu duba addini ko yaren su a yayin gudanar da ayyukan mu na bada tallafin.”

” A wannan kashin da muka kaddamar a Dutsen kura a duk abun muk rabawa yaran akwai adugar al’ada da dankamfe da Kuma rigar mama da sabulun wanka da na wanke.”

Ya Kara da cewar kungiyar ta Kuma ziyarci sansanin Yan gudun hijira dake Gusoro a karamar hukumar Shiroro da Kuma kafin Koro dake karamar hukumar Paikoro inda sama da makarantu 60 suka anfana da karamcin kungiyar.

Rev Father Chiedozie ya ce “a wannan kashin Muna da yara 368 da zasu anfana da shirin tallafin karatun.”

Rev Father Chiedozie Ezeribe ya Kuma ce kungiyar zata Kuma sake duba wasu garuruwan kamar su yankin maikunkele, Chanchaga da mutun Daya da Kuma Gbaiko.

A sakon sa babban Bishop na Minna Most Martins Uzoukwu Wanda ya wakilcin sakataran ilimi na cucin Dioceses Rev Isaac Abba ya yabawa kungiyar inda ya ce hakan zai taimakawa yaran da Kuma Kara share masu hawaya kan irin halin da suke ciki.

Darakta Mai kula da Cigaban mata da yara kananana a Ma’aikatan harkokin mata ta jihar Neja Mrs Maria Ndako ta bukaci kungiyar da ta Yi kokarin Sanya Maza cikin tsarin taimakon su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *