Gwamnatin jihar Kebbi ta raba kayan abinci ga gidaje akalla tara wadanda ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kai wa hari a karamar hukumar Shanga ta jihar.
Da yake raba kayayyakin ga gidajen da abin ya shafa a kauyen Tunga Makera da ke karamar hukumar Shanga, Gwamna Nasir Idris ya nuna rashin jin dadinsa kan harin.
Idris wanda ya ziyarci kauyen, ya jajanta wa iyalai da abokan arziki da daukacin al’umma kan abin da ya bayyana a matsayin harin da bai dace ba, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen yaki da miyagun laifuka domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
Gwamnan ya samu rakiyar mai martaba Sarkin Yauri, Dr Mohammad Zayannu Abdullahi, domin jajanta wa mutanen kauyen da abin ya shafa.
Gwamnan ya kuma jajanta wa Sarkin game da rashin tsaro da ake ci gaba da yi a yankin sa tare da bada tabbacin hadin gwiwa da jami’an tsaro domin kawo karshen wannan mummunar barna.
“Zan baiwa jami’an tsaro dukkan goyon bayan da suka dace domin ganin an shawo kan matsalar da ke faruwa a fadin jihar musamman a Masarautar Yauri da Zuru inda lamarin rashin tsaro ya fi kamari,” inji shi.
Sai dai ya yaba da kokarin rundunar sojin Najeriya da sauran jami’an tsaro a jihar bisa gaggarumin atisayen da suka yi wanda ya kai ga kubutar da wasu da aka yi garkuwa da su.
Shi ma da yake nasa jawabin, mai martaba sarkin Yauri mai daraja ta daya, ya gode wa gwamnan bisa wannan ziyara da ya kai masa, inda ya ce: “Wannan shi ne karo na farko da za mu ji tasirin gwamnati”.
“Mutanena sun fuskanci kalubalen tsaro da dama; muna matukar bukatar goyon bayan gwamnati da hukumomin tsaro domin baiwa mutane damar barci da idanunsu biyu da gudanar da aikin nomansu da sauran sana’o’insu cikin lumana,” Abdullahi ya bukaci.
Leave a Reply