Majalisar dokokin jihar Gombe ta amince da tsawaita wa’adin aiki tare da sake nada shugabannin riko na kananan hukumomi goma sha daya daga watan Yuni zuwa Disamba 2023.
An bayar da amincewar ne bayan an gama tattaunawa a zaman na musamman kan wasikar da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya aike wa majalisar.
Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Yamaltu ta gabas, Mista Adamu Saleh Pata, wanda ya gabatar da kudirin, ya ce akwai bukatar a ci gaba da gudanar da harkokin mulki, don haka ya bukaci ‘yan majalisarsa da su ba shi amincewa cikin gaggawa.
Leave a Reply