Take a fresh look at your lifestyle.

Gamayyar Masu Ruwa Da Tsaki Akan Harkokin Ilimi Sun Goyi Bayan Gwamnan Kano Akan Rusau

1 314

Gamayyar masu ruwa da tsaki kan harkokin ilimi a jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya da ya hadar da malamai daga kwalejojin ilimi da na fasaha a jihar karkashin jagorancin Injiniya Dakta Ibrahim Usman Aikawa ta nunar da takaicinta kan yadda gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta kacaccala filayen makarantu da dama a Kano wadanda aka tanada don amfanin gobe aka siyar da su ga masu hannu da shuni da gamayyar ta bayyana su a matsayin marasa kishin ilimin jihar ta Kano.

 

A taron manerma labarai da gamayyar ta kira a wannan Laraba a Kwalejin fasaha ta jihar Kano, jagoran zaman Injiniya/Dakta Ibrahim Usman Aikawa, yace matakin gwamnatin Kano na rushe gine-ginen abu ne mai kyau duk da cewa akwai wadanda suka fito suna kokawa da kwace masu filin wanda a cikinsu har da wanda yace ya kashe kudi kimanin miliyan dari takwas adadin kudin da a cewarsa wanda ke da su da wahala ya kai yaransa makarantar gwamnati da ke zama wacce talakawa suka fi amfana. Sai dai don bukatar kansa filin da dubban yara za su amfana ya bi hanyar da ta haramta ya mallaka.

 

Har ila yau Injiniya Aikawa yace suna goyon baya dari bisa dari kan matakan da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ke dauka na rushe gine-ginen (gidajen kwana da shaguna da wuraren biki da wurin wasanni) da aka yi ba bisa ka’ida ba a makarantun jihar, abin da ke zama barazana ga makomar yara masu tasowa da ke halartar makarantun gwamnati a jihar.

 

Wasu daga cikin makarantu a Kano da suka fuskanci kutse da kwace filayensu a gwamnatin da ta gabata don bukatar wasu daidaiku sun hadar da; 1. Gidan Sarki Primary School, Dorayi Karama 2. Goron Dutse secondary school, Layin WRECA 3. Northwest University 4. Kano State Polytechnic 5. Aminu Kano College for Islamic and Legal Studies 6. Dawakin Dakata Primary School 7. Alfijir Science Secondary School 8. First Lady Secondary School baya ga saura.

 

Gamayyar masu ruwa da tsakin kan ilimi a jihar ta Kano dai ta nemi gwamnan Kano ya dauki wadannan matakai;

 

1.Kada ya saurari masu kiran ya dakatar da aikin rushe wuraren da marasa kishi suka kwace wa makarantu suka yi gine-gine don rashin kishin bangaren ilimi, kazalika kada ya damu da masu suka da gamayyar ta bayyana su da zama ‘yankore.

 

Cikin gaggawa a samar da wata matsaya da za ta samar da kariya ga wuraren al’umma a taka birki ga daidaikun mutane da ke son mayar da wuraren al’umma su zama nasu. Wannan zai sa al’umma su rika ba da kariya ga kadarorin gwamnati sanin cewa na al’umma ne.

 

 

Daga lokaci-zuwa lokaci gwamnan ya rika jagorantar wayar da kan Kanawa da wadanda ke da zaune tare da su su sani cewa baa daukar wuraren da al’umma ke amfani da su a ba wa mutum guda don bukatar kai.

 

Taron manema labaran dai ya samu halartar masana a fannin na ilimi da dalibai da ke kallon karbe wuraren da magabata suka yi masu tanadi a fannin na ilimi shekaru masu yawa da ke tafe abin takaici, kana suna fatan gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta kawo karshen kwace filayen makarantu a jihar don ilimi ya ci gaba da samuwa a tsakanin marasa karfi da ke da rinjaye a jihar ta Kano.

One response to “Gamayyar Masu Ruwa Da Tsaki Akan Harkokin Ilimi Sun Goyi Bayan Gwamnan Kano Akan Rusau”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *