Take a fresh look at your lifestyle.

Kakakin Majalisa Ya Koka Da Ambaliyar Ruwa A Abuja, Ya Yi Kira Da A Dau Mataki

0 108

Kakakin majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abbas (PhD) ya koka da yadda ambaliyar ruwa ta mamaye rukunin gidaje na Trademore, Lugbe, Abuja, wanda ya yi sanadiyar salwantar dukiya ta miliyoyin naira.

 

 

 

Dokta Tajudeen Abbas ya ce abin takaici ne matuka yadda mutane ke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullun tare da iyalansu sun samu kansu cikin wannan mawuyacin hali.

 

 

 

Shugaban majalisar ya jajanta wa mazauna unguwar Trademore game da wannan mummunan lamari.

 

 

 

Ya tuna cewa hukumomin gwamnati da abin ya shafa kafin damina sun sanar da jama’a kan yiyuwar afkuwar ambaliya a wasu sassan kasar nan, yana mai cewa wajibi ne jama’a su bi irin wannan gargadin.

 

 

 

Kakakin majalisar Abbas ya yi kira ga mahukunta da su kara kaimi domin dakile sake afkuwar lamarin.

 

 

 

Ya kuma nanata bukatar jama’a da su dauki dukkan matakan da suka dace domin kaucewa wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa.

 

 

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta babban birnin tarayya Abuja (FEMA) a ranar Juma’a ta ce mutane 116 ne ambaliyar ta shafa.

 

Ladan Nasidi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *