Take a fresh look at your lifestyle.

GASAR WASANNIN KASASHE RENON INGILA: NAJERIYA TAZO TA 7th A TEBURIN ZAKARU

0 132

Najeriya itace ta bakwai (7th) a teburin lambobin yabo a wasannin tsre-tsere da tsallake tsallake na gasar kaashe renon Ingila da aka gudanar a Birnin Birmingham 2022 , inda Najeriya ta samu lambobin yabo 35 a rawar gani da suka taka a gasar wasanin.

Ese Brume ‘yar wasan Najeriya ta burge  a rana ta goma 10 da fara was an inda ta lashe was an tazo ta daya da lambar yabo ta Zinari a filin wasanni nan tsallake-tsallake na Mata a Alexander.

A sauran wasannin kuwa ranar Lahadi,’yar tseren Najeriya Elizabeth Oshoba ta lashe lambar Azufa aDamben nauyin kilogram 54kg-57kg.

Tawagar ‘yan was an Najeriya ta lashe Zinari 12 , Azurfa 9 da Tagulla 14 a gasar wasannin tsere da tsallake-tsallake na matan kasashe renon ingila da aka gudanar  2022 a birnin Birmingham.

‘Yan wasan Najeriya sun taka tawara gani a teburin kyaututtuka akan wasannin tsallake –tsallake da tserarra da Kokawa.

 

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *