Take a fresh look at your lifestyle.

Mukaddashin Shugaban ‘Yan Sanda Yayi Alkawuran Inganta Haɗin Kai Tsakanin Cibiyoyin Tsaro

0 240

Mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Olukayode Egbetokun ya yi alkawarin inganta hadin kai a tsakanin hukumomin tsaro ta hanyar karfafa nasarorin da aka samu ya zuwa yanzu a tsarin tsaro na cikin gida na kasar.

 

Mukaddashin sufetan ‘yan sandan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu a ofishin sa.

 

 

Sanarwar ta fito ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, wanda ya ce IGP din ya samu rakiyar jami’an DIG, Adeleke Adeyinka Bode, mni; DIG Horo da Ci Gaba, Bala Ciroma; AIG Force Intelligence Bureau, Abdulyari Lafia; Sakataren rundunar, AIG Habu Sani; Daraktan Cibiyar Laifukan Intanet ta Kasa, DCP Uche Ifeanyi; da jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi.

 

A nasa jawabin, NSA, ya bayyana jin dadinsa da irin cigaban da mukaddashin IGP ya yi wajen tsaftacewa da kuma sake fasalin tsarin ‘yan sanda a Najeriya; cewa IGP ya sa kafar dama a gaba tun daga farko.

 

Mista Ribadu, ya bukaci Ag. IGP ya ba da fifikon inganta hadin gwiwa da sauran Hukumomin Tsaro don cimma burin gwamnati mai ci yayin da ya yi alkawarin bayar da cikakken goyon bayansa don ganin an samar da ingantacciyar ‘yan sanda da inganta tsaro ga kowa da kowa a Najeriya.

 

Mukaddashin IGP din ya taya NSA murna bisa cancantar nadin da aka yi masa tare da amincewa da tabbacinsa na tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasa ta hanyar diflomasiyya tsakanin hukumomi da kuma tsarin tsaro na bai daya.

 

 

 

L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *