Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu ya kaddamar da sabbin kwamishinoni 20 da aka nada, wadanda za su zama majalisar zartarwa ta jihar.
Gwamnan, a nasa jawabin, a ranar Alhamis ya umarce su da su gaggauta zuwa bakin aiki, domin gwamnati na gaggawar cika alkawuran da ta dauka a yakin neman zabe.
KU KARANTA KUMA: Gwamna Ya Mika Karin Jerin Kwamishinoni Zuwa Majalisar Enugu
Sabbin kwamishinonin da aka rantsar sun hada da Farfesa Ndubueze Mbah, Mrs Ngozi Enih, Mista Lawrence Ezeh, Farfesa Sam Ugwu, Chika Ugwoke, Dr Kingsley Udeh da Farfesa Emmanuel Obi.
Sauran sun hada da Mista Okey Ogbodo, Dame Ugochi Madueke, Lloyd Ekweremadu, Gerald Otiji, Nathaniel Uramah, Dr Malachy Agbo da Mista Aka Eze Aka.
Sabbin kwamishinonin sun kuma hada da Mrs Adaora Chukwu, Dr Martin Chinweike, Obi Ozor, Emeka Ajogwu, Chris Robert Ozongwu, Dr Felix Nnamani da Patrick Ubro.
Gwamnan ya jaddada kudirin sa na habaka tattalin arzikin jihar nan, da gaggauta samar da ababen more rayuwa da tattalin arziki, da kuma ci gaban jama’a a jihar.
Mbah ya ce sabbin kwamishinonin sun fito ne daga kwarya-kwaryar neman nagartattun hannaye don taimakawa gwamnatinsa wajen gabatar da takardar ta.
“Mun bayyana wani gagarumin hangen nesa da zai sa mu bunkasa tattalin arzikinmu yadda ya kamata. Mun kuma yi wa al’ummarmu alkawarin kawar da fatara da kuma son sanya jihar Enugu ta zama farkon wurin zuba jari.
“Waɗannan ra’ayoyi ne abin yabo da ɗaukaka. Amma lokacin da muka yi wadannan alkawurra, muna bukatar tawagar da za ta isar da mutanenmu daga inda muke a yau zuwa inda muke son kai su.
“Saboda wannan, tsarin da ya haifar da zaɓin ku ya kasance mai tsauri kuma dalla-dalla.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply