Take a fresh look at your lifestyle.

Kwamandan Rundunar Sojoji Ya Tantance Ci Gaba Akan ‘Yan Boko Haram

0 108

Kwamandan rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF), Manjo Janar Ibrahim Ali, ya tantance irin ci gaban da ake samu a yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram a Najeriya.

 

Jami’in yada labarai na rundunar soji a N’djemena, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi wanda ya bayyana hakan ta shafin Twitter na rundunar sojin Najeriya ya bayyana cewa, kwamandan rundunar ya yi wannan tantancewar ne a lokacin da ya ziyarci sashe na 3 Monguno a Najeriya.

A yayin ziyarar tasa, Kwamandan rundunar ya yabawa bangaren bisa namijin kokarin da suke yi na ganin an samu nasarar aikin MNJTF, inda ya yabawa sojojin bisa kwazon da suke yi.

 

 

Manjo Janar Ali ya bukaci sojojin da su ci gaba da kokarin kawar da sauran ‘yan ta’addan na Boko Haram.

 

Ya kara da cewa mika wuya da mayakan na Boko Haram suka yi a baya-bayan nan wata manuniya ce da ke nuni da cewa yakin da ake yi da kungiyar ya kusa kawo karshe.

 

Kwamandan rundunar ya shawarci jami’an da su kasance da tunani mai kyau a yayin gudanar da ayyukansu, inda ya bayyana cewa kokarin da suke yi ya taimaka matuka wajen ci gaban da aka samu a yaki da ‘yan ta’adda.

 

Manjo Janar Ali ya bayyana godiyarsa ga “Rundunar hadin gwiwa ta farar hula” bisa gagarumin tallafin da suka bayar.

 

Ya kuma fahimci irin rawar da al’ummar yankin ke takawa wajen samar da muhimman bayanai da taimako wajen yakar Boko Haram.

 

A cewar kwamandan rundunar, hadin kan fararen hula na da matukar muhimmanci wajen kawo karshen ta’addancin da kungiyar ta’addanci ta haddasa.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *