Majalisar Zartaswa ta amince da kudi Naira Biliyon N43 domin shinfida hanyoyi a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya.
Ministar Jinkai da ci gaben harkokin rayuwa, Sadiya Farouk, ta sanar da haka jim kadan da kamala taron hukumar raya yankin Arewa Maso Gabashi ce Zata kula da aiyyukan.
Farouk tace jihohin da asu ci gajiyar aikin sune Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe da Yobe.
Tace: “Yau, Maaikatar Jin kai da Rayuwa ta gabatar wa Majalisa a madadin Hukumar Raya yankin arewa maso gabashi Bukatu hudu.wadannan sun hada da shinfida hanyoyi a jihohi biyar a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya,wanda ya hada da Barno, Yobe, Adamawa, Gombe and Bauchi.
“A Barno, muna da hanya mai tsawon kilomita 22.5 da ake shinfidawa. Wannan sune Ngon-Koshode da Ngon-Dosmari-Zabamari-Kongologo-Kajari inda Zasuci kudi naira N13,553,902,668.95
Hanya ta biyu itace kilomita 53 wato daga Gombe-Abba Zuwa Kirffi a Gwambe da Bauchi Kwangilar da ata ci kudi Naira N11,697,355,449.61.Sauran hanyoyin masu kilomita 54 Mutai a hanyar Gudal a Jihar Yobe kwangilar zata lashe kudi Naira N12,199,182,845.70.
LADAN NASIDI
Leave a Reply