Take a fresh look at your lifestyle.

Jihar Neja Da Kasar Indiya Zasu Hada gwiwar Bunkasa Sashin Noma

0 167

Gwamnatin Jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya Najeriya za ta hada gwiwa da gwamnatin Indiya a fannonin sarrafa kanikancin noma da sauran ayyukan raya kasa.

Gwamnan jihar Alhaji Umar Mohammed Bago ya bayyana haka a ziyarar da ya kai wa babban kwamishinan kasar Indiya Gangadharan Balasubramanian domin neman hadin gwiwa da gwamnatin Indiya a wata alaka mai amfani da juna a Abuja babban birnin Najeriya.

 

Gwamnan a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Bologi Ibrahim ya fitar, ya kuma tattauna kan samar da rance daga gwamnatin Indiya don siyan injinan noma na zamani domin bunkasa harkar noma a jihar.

 

Gwamnan jihar Neja wanda kuma ke neman gwamnatin Indiya ta shiga cikin harkokin koyo da koyarwa, ya bayyana aniyarsa ta gina daya daga cikin asibitocin koyarwa mafi inganci a Najeriya domin kula da lafiyar al’ummar jihar da ma sauran su.

 

Da yake mayar da martani, babban kwamishinan Indiya, Gangadharan Balasubramanian ya bayyana shirin gwamnatin Indiya na hada kai da gwamnatin jihar Neja.

 

Babban Kwamishinan na Indiya ya kuma bukaci gwamnatin Jihar Neja ta yi amfani da damar da ake da ita na dangantakar da ke tsakanin Najeriya da gwamnatocin Indiya, domin samun lamuni na ayyukan cikin gida daga gwamnatin Indiya da za a biya nan da shekaru goma.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *