Gwamnatin Jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta ce zata samar da motoci da suke anfani da gas domin saukakawa alumma irin halin damuwa da suke ciki.
Gwamna jihar Umar Muhammad Bago shine ya bayyana hakan a bikin rantsar da sabbin kwamishinoni da manyan masu bashi shawara da da kuma manyan sakatarore uku a dakin taro na Legbo Kutigi dake Minna .
Gwamna Umar Mohammed Bago ya ce wannan matakan da gwamnatin jihar zata dauka zai rage irin wahalhalu da kuncin rayuwa da alumma suka tsinci kansu sakamakon cire tallafin mai da gwamnatin Tarayya tayi.
Har ila yau gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta himmatu wajan ganin ta samar da yanayi mai kyau ga alummar jihar musammam wajan kawo karshen matsalar tsaro da ke neman dai daita wasu yankunan jihar, inda ya ce tuni ya kirkiro da Ma’aikata ta musamman don kula da makiyaya da ilmantar da ya’yan su, kana a janyo su cikin alumma.
Gwamna Umar Muhammad Bago ya kara da cewar, gwamnati zata samarwa da alummar jihar karin tallafi da zai Kara Saukaka walwala a tsakankanin su ganin cewar tallafin gwamnatin taraya ba kowane lokaci zai rika zuwa ba.
Ya kuma shawarci sabbin kwamishinoni da masu bashi shawara da su rika ziyartar yankunan su domin kara baiwa alummar kwarin gwiwa kan manifofin gwamnati mai ci na kawo cigaba mai daurewa a jihar Neja.
A jawabin sa a madadin sauran kwamishinonin da manyan masu bada shawara, Barista Morice Bello Magaji wanda shine kwamishinan Filaye da safayo, ya yabawa Gwamnan bisa duba chanchanta da yayi na zabo au domin au bada tasu gudumuwar wajan ciyar da jihar gaba, inda ya baiwa Gwamnan tabbacin yin aiki tukuru don ganin basu bashi kunya ba.
Barista Morice Bello Magaji ya kara da cewar zasu mutunta tsare tsaren da Gwamnan Umar Mohammed Bago ya bullo da su don taimakawa jihar Neja .
Wasu daga cikin wadanda suka halarci bikin har da kungiyar masu bukata ta musamman, inda suka nuna goyan baya su kan irin manufofi da kudirin gwamnatin mai ci, kana suka Yaba da yadda Gwamnan ke kokarin ganin ya shigo da su gwamnati don suma su bada tasu gudumuwa na gina jihar.
Yakubu Salihu Abdullahi shine jagoran masu bukata ta musamma da suka halarci bikin rantsar da kwamishinonin da masu bada shawara, ya kuma bayyana cewar Gwamnan ya sha alwashin basu mukamai a gwamnatin sa.
Hakaalika a kwannan ne Gwamnan Umar Muhammad Bago ya baiwa wasu mata su 131 mukaman masu bashi shawara domin cika alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.
An rantsar da kwamishinoni 30 da masu bai wa Gwamna shawara na musamman 30,sakatarorin Dindindin 5 da wakiliyar babbar alkalin alkalan jihar Justice Halima Abdulmalik ta rantsar.
Nura Muhammed.
Leave a Reply