Take a fresh look at your lifestyle.

Niger Za Ta Bada Dama Ga Wasu Sojojin Junta

0 107

Jagoran juyin mulkin jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya rattaba hannu kan wata doka da ta bai wa ‘yan uwan ​​gwamnatocin sojojin Mali da Burkina Faso damar tura dakarunsu cikin kasarshi domin su taimaka wajen kare kai harin.

 

An bayyana hakan ne bayan ministocin harkokin wajen Burkina Faso, Olivia Rouamba, da Mali, Abdoulaye Diop, sun ziyarci Janar Tchiani a Yamai ranar Alhamis.

 

Kungiyar kasashen yammacin Afrika ta Ecowas ta yi barazanar yin amfani da karfi wajen maido da zababben shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum bisa tafarkin dimokuradiyya, wanda wasu gungun hafsoshin soji suka sauke a watan jiya.

 

Tana kokarin yin shawarwari da shugabannin juyin mulkin amma ta yi gargadin a shirye ta ke ta aika da sojoji idan diflomasiya ta gaza.

 

BBC/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *