Take a fresh look at your lifestyle.

Shugabar Kasar Taiwan Zata Ziyarci Kawayen Afirka na Karshe Eswatini

0 110

Shugabar kasar Taiwan Tsai Ing-wen za ta ziyarci Eswatini a wata mai zuwa, wadda ita ce kawarta daya tilo a Afirka, a kokarinta na karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.

 

Za ta halarci bukukuwan murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kan kasar da kuma ranar haihuwar Sarki Mswati III yayin ziyarar.

 

Ziyarar ta na tsakanin 5 zuwa 7 ga Satumba, za ta kuma cika shekaru 55 na dangantakar kasashen biyu.

 

Kasar Sin tana ikirarin kasar Taiwan a matsayin kasarta da ba ta da hurumin hulda tsakanin kasa da kasa. Tana da alaka a hukumance da kasashe 13 kacal ciki har da Eswatini.

 

An jiyo mataimakin ministan harkokin wajen kasar Taiwan Roy Lee yana shaidawa manema labarai cewa ziyarar ta shugaban kasar ta Taiwan ba wai don yin gogayya da ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a makwabciyarta Afirka ta Kudu a wannan mako ba.

 

Madam Tsai ta ziyarci Eswatini a shekarar 2018. Ita ce kasa daya tilo daga Afirka da ke kulla huldar diflomasiyya da tsibirin Asiya bayan da Burkina Faso ta koma China a watan Mayun 2018.

 

BBC/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *