A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu ne ke jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya na farko, FEC, na wannan gwamnati mai ci.
Taron dai yana gudana ne a zauren majalisar dokoki a Fadar Shugaban Kasa Abuja.
An rantsar da sabbin ‘yan majalisar ministocin ne a ranar Litinin din makon da ya gabata, bayan da majalisar dattawa ta tabbatar da su kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Majalisar ministocin ta kunshi ministoci 45 da suka yi nasara lokacin da aka tantance su yayin da aka ki amince wasu uku.
Haka kuma mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima; Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume; Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folashade Yemi-Esan da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila sun halarci taron.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a wajen rantsar da Ministoci a ranar 21 ga watan Agusta, inda ya jaddada cewa, “mafi girman aikin da suke da shi shi ne su maido da imanin jama’a a cikin gwamnati, ta yadda jama’a za su sake yarda cewa na hannun daman gwamnati za su iya yin aiki.”
Ya kuma bukaci Ministocin da su yi aiki cikin gaskiya, da mutunci, kuma su yi aiki, yana mai jaddada cewa, “zai rike su a matsayin abin da ‘yan Najeriya ke bukata.”
Kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, Majalisar Dattawa ta tantance tare da tabbatar da Ministoci 45 da za su kula da ma’aikatun gwamnatin Najeriya a wannan gwamnatin na sabon fata.
Ladan
Leave a Reply