Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai gabatar da jawabi a taro karo na 78 na babbar muhawarar babban taron Majalisar Dinkin Duniya, UNGA, a hedikwatar MDD dake birnin New York a ranar Talata, 19 ga watan Satumba.
Shugaba Tinubu ne zai kasance shugaban Afrika na biyar da zai yi jawabi a ranar daya ga taron, kamar yadda jerin sunayen masu magana da yawun ofishin shugaban Majalisar suka nuna.
A cikin jerin sunayen, Mista Tinubu zai kasance mai magana na 14 a cikin shugabannin 20 da aka shirya yin jawabi a ranar farko.
Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, mai magana na 10, zai kasance shugaban Afrika na farko da zai yi jawabi a zaman safiya na Majalisar.
A zaman da za a yi na tsakar rana, ana sa ran shugabannin Afirka biyar za su yi jawabi a wurin taron.
Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ne zai zama shugaban Afrika na farko da zai yi jawabi a zaman na yammacin ranar, sai kuma shugaban Moroko Aziz Akhannouch da shugaban Mozambique Filipe Nyusi.
Macky Sall, shugaban kasar Senegal, zai kasance mai jawabi na biyar na Afirka da zai halarci taron, inda ya kammala jawabin bude taron ranar bude taron.
Luiz da Sliva, shugaban Brazil, zai jagoranci shugabannin duniya wajen gabatar da jawabinsa a zaman taro na 78, sai kuma shugaban Amurka Joe Biden, mai jawabi na biyu na al’ada a matsayin mai masaukin baki.
Za a fara taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 (UNGA 78) a ranar Talata 5 ga Satumba, tare da rantsar da sabon shugaban kasa, Dennis Francis na Trinidad da Tobago, wanda zai jagoranci zaman na tsawon watanni 12 masu zuwa.
Taron wanda aka shirya daga ranar 19 ga watan Satumba zuwa 29 ga watan Satumba, babban taron muhawarar zai gudana ne a kan taken sake gina amana da sake farfado da hadin kan duniya, da gaggauta daukar matakai kan ajandar 2030 da manufofinsa masu dorewa, da nufin samar da zaman lafiya, wadata, ci gaba, da dorewar duniya baki daya.
Afirka New YorkPBAT Ladan
Leave a Reply