ππ¬ππππ π±π¬π¬,π¬π¬π¬ ππ π¦π¨ ππ πππ‘π ππ π§πππππππ‘ ππͺππ π‘ππ§ππ‘ πππ‘π’
Yusuf Bala Nayaya, Kano
A kokarinta na ganin ta rage wa alβumma radadin da suke ji dalilin cire tallafin manfetir da ma cika alkawuran da ta daukarwa alβumma a ranar Litinin dinnan Gwamnan Kano Abba Kabir Yusf ya jagoranci kaddamar da aikin rarraba kayan tallafi ga magidanta 500,000 da ma ba da tallafi aikin gona a shirin da ya kaddamar a shalkwatar Hukumar kula da ayyukan Gona da raya Karkara ta jihar (KNARDA).
Gwamnan yace wannan tallafi zai kai ga mutanen da suka fi bukata a yankunan karkara da birane a fadin jihar kuma zai taimaka masu ba kawai rage radadin cire tallafin manfetir ba har ma da kokari da gwamnatin jihar ke yi na yaki da talauci a tsakanin alβumma.
A cikin jawabinsa a yayin taron gwamnan yace za a rarraba shinkafa mai nauyin kilogram goma guda 297,000, haka nan zaa rarraba buhun masara mai nauyin kilogram goma gudaΒ 160,000 zuwa ga mabukata a daukacin kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar ta Kano.
Domin tabbatar da ganin kayayyakin sun kai ga iyalan da aka tsara za a ba wa za a kai kayan zuwa ga mazabu 484 na jihar. Kowace mazaba za ta samu buhunhuna 565 na shinkafa mai nauyin kilogram 10 ga masara buhu 330 mai nauyin kilogram 10.
An kuma zabi wuraren da za a rarraba wannan tallafi kamar haka: gidajen gajiyayyu da cibiyoyin kula da alβumma da masu bukata ta musamman da makarantun Tsangaya da Islamiyoyi da wasu asibitoci da aka zaba da kananan maβaikata na gwamnati a takaice dai kayan tallafin za su dangana ga magidanta 500,000 a fadin jihar ta Kano a cewar Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Don tabbatar da ganin an yi adalci wajen rabon kayan tallafin gwamnati ta samar da kwamitoci a matakan jiha da kananan hukumomi da mazabu da za su sa idanu don tabbatar da ganin an kai wannan tallafi ga iyalan da aka tsara za a bawa.
Yusuf Bala Nayaya, Kano
Leave a Reply