Gwamnatin jihar Katsina tayi hadin gwiwa da hukumar raya kasashe ta majalisar dinkin duniya (UNDP) domin tallafama wadanda matsalar tsaro ta shafa a jihar
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ne ya bayyana hakan a birnin Katsina a wajen taron manema labarai na cikar sa kwana 100 a matsayin gwamnan jihar
Dikko Radda ya bayyana cewa daga cikin ayyukan da za’a gudanar kalkashin hadin gwiwar akwai gina gidaje a wasu yankunan da lamarin tsaron ya faru domin samar da ingantaccen muhalli ga wadanda matsalar tsaron ta rabo da gidajen su
Yace za’a fara yin gwaji na ginin gidajen a karamar hukumar jibia wadda ke d’aya daga cikin ‘kananan hukumomin da kauyukan ta ke fama da matsalar tsaron
Kazalika yace daga cikin ayyukan da jarjejeniyar zata aiwatar akwai horas da Yan gudun hijirar sana’o’i tare da tallafa masu da jari domin inganta tattalin arzikin su
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na cigaba da d’aukar matakan da suka wajaba da nufin kawo karshen matsalar domin maido da zaman lafiya a fadin jihar
Daga cikin matakan da gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin tana dauka wajen tunkarar matsalar domin magance ta akwai shirin daukar daruruwan matasa a yankunan da ake fama da matsalar tare da koyar da su dabarun tsaro domin maido da tsaron a yankunan da suka fito
Yace a yanzu haka ana kan horar da matasan kuma an tanadi kayan aiki wadanda da zaran an kaddamar da su nan bada jimawa ba za’a tura su a yankunan da suka fito domin tsare al’ummar su tare da tabbatar da kawo karshen matsalar tsaron
Dag nan sai gwamnan ya jaddada bu’katar da ake da ita ga al’ummar jihar na tallafawa shirye shirye da tsare tsaren ta domin ciyar da jihar gaba
Yana mai bada tabbacin gwamnatin na karbar gyara ko shawarwari daga garesu a inda ya kamata domin cimma nasarar da ake bukata.
Kamilu Lawal.
Leave a Reply