Take a fresh look at your lifestyle.

CAN A Jihar Neja Ta Bukaci Gwamnati Ta Dauki Karin Malamai Don Koyar Da Darasin Addini

Nura Muhammed,Minna.

0 141

Kungiyar kristoci ta kasa a Najeriya CAN, reshin jihar Neija dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta bukaci gwamnati jihar Neja da ta taimaka don daukan   malaman da zasu  koyar da darasin addinin Krista na CRK  a makarantun gwamnati.

 

Shugaban kungiyar kristocin a jihar Neja Rev Dr. Bulus Damuwa Yahanna shine ya bukaci hakan a wajan Taron koli na Shugabannin kungiyar CAN na NACREN da ya gudana a Minna fadar gwamnatin jihar Neja.

 

Rev Dr Bulus Damuwa Yahanna ya ce ” koyar da darasin zai taimaka wajan koyar  da tarbiya  da sanin kimar alumma musamman ga mabiya adinin.”

 

Shugaban ya Kara da cewar an Dan sami koma baya wajan samun kwararrun Malamai da ke koyar da darasin Wanda hakan ya Sanya mafi yawanci daliban da suka kammala karatun su Basa iya fahimtar irin mahimmancin dake tattare da koyarwar addini Krista.

 

” Darasin na taimakawa wajan fahimtar da dalibai da Kuma koyar da su ka’idoji da dokokin adinin domin zama alumma ta gari.” Rev Dr Bulus Damuwa Yahanna.

 

Tun da farko a jawabin sa Shugaban kungiyar NACREN ta kasa Rev Dr Reuben Maiture ya bukaci gwamnatin taraya da ta baiwa darasin mahimmanci domin a sami nasarar koyar da alumma dabi’a ta gari.

 

Ya Kara da cewar rashin isasaun malaman ne ta Sanya kungiyar Neman malaman Sakai don  koyar da darasin kyauta.

 

 

Nura Muhammed.

Leave A Reply

Your email address will not be published.