Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Kashim Shettima zai kai ziyarar aiki a jihohin Kebbi da Sokoto dake arewa maso yammacin Najeriya.
A Jihar Kebbi mataimakin shugaban kasa zai kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi malamin addinin musulunci Sheikh Abubakar Giro a garin Argungu.
Sheikh Giro, wanda ya rasu a ranar Larabar da ta gabata, ya kasance babban malamin addinin Musulunci kuma babban sakataren kungiyar Jama’atul Bidi’a Wa’ikamatul Sunnah ta kasa (JIBWIS).
Tuni dai gidan marigayi limamin da fadar Sarkin Argungu ke sanye da sabbin kayaki, inda jami’an tsaro ke ci gaba da sanya ido a cikin shirin zuwan mataimakin shugaban kasar.
Daga baya VP Shettima zai koma jihar Sokoto, domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar ya aiwatar, domin tunawa da kwanaki 100 a kan kujerar gwamnan jihar, Ahmed Aliyu, wanda ya karbi mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Mataimakin shugaban kasar zai ci gaba da kaddamar da ayyuka a Sokoto ranar Litinin, kafin ya dawo Abuja.
Leave a Reply