Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya ce duk da kokarin da gwamnatoci a matakai daban-daban ke yi, gibin gidaje a Najeriya na da yawa, inda ake bukatar Naira tiriliyan 21 don cike gibin da ya dace.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a jihar Sokoto, a wajen kaddamar da ginin rukunin gidaje 500 da gwamnatin jihar ta yi.
VP Shettima, wanda ya yabawa gwamnan jihar, Ahmed Aliyu bisa kokarin da yake yi na magance bukatun gidajen jama’ar sa, ya bayyana cewa gibin gidaje a Najeriya ya kasance babban kalubale.
A cewar VP, “Najeriya na da gibin gidaje miliyan 28 kuma za mu bukaci Naira tiriliyan 21 don biyan bukatun mu na gidaje.
“Wannan matakin da Gwamnan ya dauka abin yabawa ne kuma ya cancanci sauran gwamnatocin Jihohin su yi koyi da shi.
“Gwamnan ya fara da kyau ta hanyar kammala tituna da gadar sama da ya gada,” in ji shi.
Tun da farko a nasa jawabin, gwamna Aliyu ya ce gidan na ma’aikatan gwamnati ne kuma za a sayar musu da su idan an kammala su bisa ga magidanta.
“Wannan wani aiki ne da tsohon Gwamnan Jihar, Aliyu Magatakarda Wamakko ya kaddamar amma daga baya gwamnatin da ta shude ta yi watsi da shi amma mun kuduri aniyar kammala shi domin amfanin ma’aikatanmu da sauran jama’a,” inji shi.
Gwamnan ya bayyana cewa aikin wanda ke karamar hukumar Wamakko zai kashe gwamnatin jihar Naira biliyan 7.3 domin kammala aikin.
Taron wanda zai cika kwanaki 100 akan karagar mulki da gwamnatin ta samu halartar tsohon gwamnan jihar Sokoto Sen. Aliyu Wamakko; Ministan Noma da Abinci, Abubakar Kyari; Karamin ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli Bello Goronyo da tsohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto Mukhtari Shagari da dai sauransu.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply