Ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry ya gana da takwaransa na Faransa Catherine Colonna a birnin Alkahira jiya Alhamis.
A yayin ganawar tasu, ministocin biyu sun tattauna kan alakar kasashen Masar da Faransa, da kuma sabbin abubuwan da suka faru a yankin ciki har da batun Falasdinu.
A wani taron manema labarai na hadin gwiwa, Shoukry ya mika ta’aziyya ga al’ummar kasar Libya, wadanda a baya-bayan nan suka fuskanci ambaliyar ruwa da ta yi sanadin asarar dubban rayuka.
Ya kuma mika ta’aziyyar shi ga al’ummar Maroko, wadanda ke kokawa da mumunar girgizar kasa da ta afku a makon jiya.
A waje guda kuma, ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna ta ce “ana jin illar yakin Rasha a Ukraine a duk duniya, inda ta kara da cewa Masar ta sami matsala matuka sakamakon karuwar karancin abinci.”
Africanews/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply