Take a fresh look at your lifestyle.

Kasar Maroko Ta Bude Shirin Samar Da Gidaje Ga Yankunan Girgizar Kasa

0 104

Kasar Maroko ta sanar da kaddamar da wani shirin ba da tallafi na da kuma mayar da mazauna gidaje kimanin 50,000 da girgizar kasa ta afkawa a makon jiya.

 

Girgizar kasa mai karfin awo 6.8, wadda ita ce mafi karfi da aka taba fuskanta a kasar Maroko, ta kashe mutane kusan 3,000 tare da raunata fiye da 5,600 tun bayan da ta afku a ranar Juma’ar da ta gabata a lardin Al-Haouz da ke kudu da cibiyar yawon bude ido ta Marrakesh.

 

Wadanda aka bari ba su da matsuguni za a ba su mafaka na wucin gadi a cikin “tsarin da aka tsara don jure sanyi da mummunan yanayi, ko kuma a wuraren liyafar da ke dauke da duk abubuwan jin daɗi”, in ji ofishin masarautar a cikin wata sanarwa bayan taron da Sarki Mohamed VI ya jagoranta.

 

Sanarwar ta kara da cewa, hukumomin kasar Morocco sun kuma ba da umarnin bayar da agajin gaggawa Dirhami 30,000 (kusan dalar Amurka 3,000) ga iyalan da bala’in ya shafa.

 

Ya ce wannan zai zama matakin farko na shirin da ya shafi wasu gidaje 50,000 da suka ruguje gaba daya ko kuma a wani bangare sakamakon girgizar kasar.

 

Ba a san adadin mutanen da girgizar kasar ta bari ba tare da matsuguni ba, wanda ya lalata kauyuka da dama a yankin tsaunin Atlas na Maroko.

 

Ofishin masarautar ya ce Dirhami 140,000 kwatankwacin dalar Amurka 13,600 ne za a ware wa gidajen da suka ruguje gaba daya, baya ga dirhami 80,000 don sake gina wasu sassa da suka rushe.

 

Maroko ta bai wa kungiyoyin agaji damar kai agaji daga Spain, Birtaniya, Qatar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa, amma ya zuwa yanzu ta ki amincewa da tayin da wasu kasashe da dama da suka hada da Amurka da Faransa da wasu kasashen Gabas ta Tsakiya suka yi.

 

 

Africanews/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *