Take a fresh look at your lifestyle.

Amurka Ta Ci gaba da Anfani Da Jiragen Leken Asiri A Nijar

0 116

Shugaban Rundunar Sojin Sama a Turai da Sojojin Sama na Afirka, Janar James Hecker, ya sanar da cewa, sojojin Amurka sun fara ayyukansu a Nijar, da suka hada da anfani da jiragen sama marasa matuka da jiragen sama daban-daban daga sansanonin sojin saman kasar.

 

Wani kakakin ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon ya ce an dakatar da farmakin da sojoji suka yi a karshen watan Yuli, inda ya bayyana cewa sauran ayyukan sojojin Amurka a kasar sun samu nakasu.

 

“Za mu tabbatar da cewa sojojin Amurka a Nijar sun gudanar da leken asiri da jiragen sama domin kawar da barazanar da kuma tabbatar da tsaron sojojin mu”, in ji kakakin rundunar Pentagon ta Afirka.

 

“Mun sami izini daga hukumomin da suka dace,” in ji ta, tare da lura da cewa ” a koyaushe Amurka tana da ‘yancin gudanar da ayyuka da nufin kare sojojinmu da ma’aikatanmu, idan ya cancanta.

 

Kakakin ya ce, duk da cewa an dawo da zirga-zirgar sa ido, amma ana ci gaba da yin musanya da sojojin Nijar kamar horo ko hadin gwiwar yaki da ta’addanci.

 

Amurka na da sojoji kusan 1,100 a Nijar, wadanda ke yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda a wannan yanki.

 

Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta sanar a ranar 7 ga watan Satumba cewa tana mayar da sojojinta “a matsayin riga-kafi”, inda take tura wasu sojoji daga wani sansani a Yamai babban birnin kasar zuwa wani sansanin sojin sama da ke arewa.

 

 

Africanews/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *