Zan Tallafawa Al’ummar Mazabata Ba Tare Da Banbancin Jamiyya Ba : Hon Husaini Mai kero
Abdulkarim Rabiu, Abuja
Dan majaliar tarayyar dake wakiltar mazabar Kaduna ta kudu, Hon Hussaini Abdulkarim Ahmed wanda aka fi sani da (Mai kero) ya jaddada aniyarsa ta maida hankali wajen bunkasa rayuwar al’ummar mazabarsa ba tare da banbancin jamiyya, addini ko kabilanci ba.
Dan majalisar ya bayyana hakan ne a wani taro da ya gudanar da masu ruwa da tsaki na Jamiyyar PDP dake karamar hukumar Kaduna ta kudu domin bayyana irin tsare tsaren da ya tanadarwa alummarsa a wakilcin da yake musu a majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya.
Ya ce irin wannan zaman da masuwa da tsaki ya zama wajibi domin a cikinsu akwai masu karewa da gogewa wadanda za su ba da shawara wajen yin abin da ya kamata .
Hussaini Mai Kero ya ce “akwai tsare tsare da na ke da su da yawa, wadanda na tanadar domin a taimaki jamma, shi ne dalilin da ya sa na kirasu domin a tattauna akai. Kamar tsari na taimakon mata masu rauni wadan da za a taimaka musu da jarin Naira 20,000, wanda za a bai wa mata 2000 a karshen wannan watan”
Ya kara da cewa zai tabbatar da cewa rabon tallafin ya kai ga duk wadanda aka yi dominsu.
Yace za fara shirin daga wannan watan da muke ciki na Satumba akwai kuma wasu tsare tsare wadan da za a ci gaba da gudarwa duk wata-wata ko kuma wata biyu idan Allah ya yarda na tallafawa al’umma.
Dangane da zabubbuka dake tafe kuwa, dan majalisar ya yi kira ga yayan Jamiyyar PDP da su hada kai domin samun nasara.
Ya kuma yi kira ga matasa da zu zauna lafaya musanman a anguwan Muazu da Yantukwane, sannan ya kuma gargade su idan ba su jiba zai dauki mataki a kansu.
“Yanda wasu ward ward suka zauna lafiya ina kira ga matasanmu da zu zauna lafiya, su je su nemi sanaoi, karatu da ayyukan yi, duk inda suka ji ana bada aiki su nema, ba zabu iya baiwa kowa aiki ba, amma za mu muga kokarin da za mu muyi, muma kuma fatan su zauna lafiya domin su kasance manyan gobe”. In ji Hon. Hussaini Abdulkarim
Abdulkarim Rabiu.
Fastidious replies in return of this matter with solid arguments and explaining all about that.