Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Najeriya Za Ta Bada Muhimmanci Kan Ilimi – Minista

0 108

Ministan Ilimi a Najeriya, Farfesa Tahir Mamman ya ce daga yanzu za a ba da fifiko ga ilimin asali domin yana tasiri ga ci gaban kasa baki daya.

Ministan ya bayyana haka ne a Abuja babban birnin kasar a ci gaba da jawabinsa na zama tare da Parastatals da Hukumomi a karkashin kulawar Ma’aikatar Tarayya ta Ilimi.

A cewarsa, “matakin tushe shine bangare mafi mahimmanci a fannin wanda dole ne a inganta shi yadda ya kamata don yin tasiri mai kyau ga sauran sassan fannin da kuma ci gaban kasa baki daya.”

Mamman ya lura cewa ƙidayar jama’a mai zuwa za ta dakatar da
cece-kuce dangane da ainihin alkaluman yaran da ba sa zuwa makaranta.

Karamin Ministan Ilimi, Dokta Yusuf Tanko Sununu ya kuma jaddada cewa dole ne kowa ya tashi tsaye wajen ganin yaran Najeriya sun samu ilimin da ake bukata domin shirya su a nan gaba.

Dokta Sununu ya umurci Shugaban Hukumar UBEC da ya kai gwagwarmayar neman tallafin takwaransa zuwa kofar Gwamnonin Jihohin inda ya bayyana cewa yaron da bai yi karatu ba hatsari ne a fili ga kansa da kuma al’umma gaba daya.

Sakataren zartarwa na UBEC, Dokta Hamid Bobo ya shaida wa Ministocin cewa kasar na bukatar karin makarantu 20,000 da kuma ajujuwa 907,769 domin daukar adadin yaran da ba sa zuwa makaranta.

Sakataren zartaswar ya bayyana gibin ababen more rayuwa da kuma rashin isassun ma’aikata a matsayin wasu kalubalen da hukumar ke fuskanta a kokarinta na tabbatar da samun ingantaccen ilimi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *