Take a fresh look at your lifestyle.

Najeriya Za Ta Fara Aiwatar Da Yarjejeniyar Ta Da Kasar Cuba

0 92

Ministan kere-kere, kimiyya da fasaha na Najeriya, Uche Geoffrey Nnaji ya ce Najeriya za ta tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar da kasar ta kulla da kasar Cuba da gaske.

 

 

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar Atuora Obed, wadda ta kara da cewa ministan ya bayyana hakan a yayin taron kolin da aka gudanar a jamhuriyar Cuba, kwanan baya.

 

 

Sanarwar ta ce a yayin taron, Nnaji ya gana da ministan kimiyya, fasaha da muhalli na Jamhuriyar Cuba Elba Risa Perez kan bukatar kasashen biyu su karfafa dangantakarsu.

 

 

Ministocin biyu sun rattaba hannu kan wata takardar yarjejeniya kan karfafa ayyukan noma da kimiyya da fasaha a madadin gwamnatocin Najeriya da na Cuba.

 

 

Nnaji ya kasance a cikin tawagar kasa karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima zuwa taron shugabannin kasashen G77+ na kasar Sin, wanda shugaban kasar Cuba, Miguel Diaz-Canel ya jagoranta.

 

 

Tawagar ta kai ziyarar ban girma ga mataimakin shugaban kasar Cuba yayin taron.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *