Take a fresh look at your lifestyle.

“DUK DA HUKUNCIN KOTU BA ZA MU DAKATAR DA AYYUKAN CI GABA BA” – GWAMNAN KANO

Yuasuf Bala Nayaya,Abuja.

1 230

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa zai ci gaba da ayyuka muhimmai duk da hukuncin kotun sauraren korafe-korafen zabe inda ma ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kashe Naira miliyan dubu uku kan wasu muhimman ayyuka a jihar.

 

 

Kwamishinan yada labarai na jihar Baba Halilu Dantiye ya bayyana haka a ranar Talata yayin zantawa da manema labarai inda ya ce a wani yunkuri na nuna cewa ba za su saurara ba da ayyukan da suka sa a gaba duk da hukuncin kotun za su dora kan ayyuka da suka faro.

 

 

Cikin ayyukan da za a yi sun hadar da auren Zawara sama da dubu guda da biyan kudaden tallafin dalibai na Jami’ar Bayero Naira miliyan 712 da kudade Naira miliyan 524 na dalibai masu jarrabawar kammala sikandare.

 

 

Sauran sun hadar da biyan kudaden kwantiragi da suka makale cikin ayyukan da aka yi tsakanin 2011-2015

 

 

Har ila yau kwamishinan yayi amfani da wannan dama wajen nuna takaicinsa kan kalaman daya daga cikin alkalan kotun sauraren kararrakin zabe wato mai shari’a Benson Anya kan ‘yan siyasa masu sanya jar hula wadanda a cewar kwamishinan daliabai ne na Malam Aminu Kano kuma dangantasu da abu mara kyau da Mai Shari’a Anya yayi za su nemi hakkinsu a hukumar da ke kula da harkokin shari’a ta kasa a Najeriya NJC.

 

 

Yusuf Bala Nayaya.

One response to ““DUK DA HUKUNCIN KOTU BA ZA MU DAKATAR DA AYYUKAN CI GABA BA” – GWAMNAN KANO”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *