Take a fresh look at your lifestyle.

MAULUDI: Mataimakin Gwamnan Kano Ya Yi Kira Ga Al’umma Suyi Koyi Da Dabi’un Fiyayyen Halitta

Yusuf Bala Nayaya,Kano.

1 174
Mataimakin Gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya taya kafatanin al’ummar Musulmi na jihar Kano dama na kasa baki daya murnar zagayowar ranar tuni da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.

 

 

 

 

A cewar Gwarzo lokaci ne na ci gaba da dabbaka halaye kyawawa na Annabi Muhhamd S.A.W da samun hadin kai da kara mika wuya wajen bautar Allah SWT.

 

 

 

 

A wasika dauke da sa hannun sakataren yada labaran mataimakin gwamnan Ibrahim Garba Shu’aibu mataimakin gwamnan ya ce wannan lokaci na Mauludi lokaci ne na sake zaburar da al’umma kan koyarwar addinin Islama da ke isar da sakon zaman lafiya da kaunar juna da yin ayyuka na kwarai.

 

 

 

 

Gwarzo ya yaba wa al’ummar Musulman saboda dabbaka ayyuka da addinin Islama ya koyar da suka hadar da zaman lafiya da kaunar juna cikin al’umma. Ya kuma sake bayyana muhimmanci na rungumar  juna da mutuntawa tsakanin al’umma kamar yadda rayuwar Annabi S.A.W ta nunar.

 

 

 

 

“Yayin da muke bikin Mauludi ina kira ga al’ummar Kano su yi amfani da wannan dama wajen kara samun hadin kai da kaunar juna da juriya a zamantakewar mu da duk al’ummar da ke Kano” A cewar Gwarzo.

 

 

 

Ya kuma yi kira ga Al’ummar Musulmi da su yi addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba a jihar ta Kano dama kasa baki daya.

 

 

 

 

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa za su ci gaba da aiki tare da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da mukarraban gwamnatinsa wajen tabbatar da ganin an inganta yanayi na rayuwar al’ummar da ke jihar ta Kano.

 

 

 

 

Yusuf Bala Nayaya.

 

 

One response to “MAULUDI: Mataimakin Gwamnan Kano Ya Yi Kira Ga Al’umma Suyi Koyi Da Dabi’un Fiyayyen Halitta”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *