Take a fresh look at your lifestyle.

Maulud Nabi: Kakakin Majalisa Abbas Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Yi Koyi Da Manzon Allah

10 191

Kakakin majalisar wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya taya al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar Maulidin Manzon Allah (SAW) na bana.

 

 

A cikin sakon shi na tunawa da zagayowar ranar, Abbas ya bukaci mabiya addinin Musulunci da su yi koyi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, yana mai cewa rayuwarsa da koyarwarsa za su ci gaba da zaburar da al’ummomi masu zuwa.

 

 

Ya ce wannan lokacin yana bukatar a yi tunani a hankali kan rayuwa da zamanin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah, wanda ya ce shi ne dan Adam mafi son zaman lafiya da ya taba rayuwa a doron kasa.

 

 

Shugaban Majalisar ya bukaci ba Musulmi kadai ba, har ma da daukacin ‘yan Nijeriya da su yi koyi da kyawawan dabi’u kamar sadaka, yafiya, gaskiya da kishin kasa, yana mai cewa wadannan suna daga cikin halayen da ya kamata shugabanni da mabiya su kasance su samu zaman lafiya da ci gaba a kasarsu.

 

 

Shugaban majalisar Abbas ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan damar wajen yi wa shugabanninsu na siyasa da na addini da na gargajiya addu’a, yayin da ya bayyana fatan addu’o’i da hadin kan masu ruwa da tsaki za su fitar da kasar nan daga cikin kalubalen da take fuskanta.

 

Ya kuma yi wa al’ummar musulmi fatan samun nasarar gudanar da bukukuwan karamar Sallah kamar yadda ya yi kira da a gudanar da zaman lafiya a wannan lokacin.

 

 

Ladan Nasidi.

10 responses to “Maulud Nabi: Kakakin Majalisa Abbas Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Yi Koyi Da Manzon Allah”

  1. It’s a shame you don’t have a donate button! I’d without a doubt donate to this brilliant blog! I guess for now i’ll settle for bookmarking and adding your RSS feed to my Google account. I look forward to new updates and will share this website with my Facebook group. Talk soon!

  2. Write more, thats all I have to say. Literally, it seems as though you relied on the video to make your point. You obviously know what youre talking about, why waste your intelligence on just posting videos to your site when you could be giving us something informative to read?

  3. Write more, thats all I have to say. Literally, it seems as though you relied on the video to make your point. You definitely know what youre talking about, why throw away your intelligence on just posting videos to your blog when you could be giving us something enlightening to read?

  4. Hi, I think your site might be having browser compatibility issues. When I look at your blog in Opera, it looks fine but when opening in Internet Explorer, it has some overlapping. I just wanted to give you a quick heads up! Other then that, superb blog!

  5. Wow, awesome blog layout! How long have you been blogging for? you make blogging look easy. The overall look of your web site is wonderful, let alone the content!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *