Majalisar Wakilai ta umurci kwamitinta mai kula da babban birnin tarayya Abuja da ya hada kai da hukumar gudanarwar babban birnin tarayya Abuja domin ganowa tare da warware duk wasu matsalolin da suka shafi rashin bayar da takardar shaidar mallakar Muhalli a babban birnin tarayya Abuja.
Wannan kuduri ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa Hon. Sada Soli, a zauren majalisa ranar Talata.
Dan majalisar ya bayyana cewa, Ministan Babban Birnin Tarayya na wancan lokacin, a shekarar 2000, ya kaddamar da shirin samar da gidaje masu inganci da araha da kuma dinke barakar gidaje ta hanyar tsarin manufofin hadin gwiwa na gwamnati da masu zaman kansu (PPP).
Ya nuna damuwarsa cewa masu kadarorin da ke cikin Matsugunan Gidajen Mass Housing Estates ba su da wata takardar shaidar zama da aka ba su a daidaikunsu domin ana ba su takardar shaidar zama ta bai daya domin mallakar kadarorin, wanda ya saba wa ka’idojin kare masu haya.
“Tsarin samar da gidaje masu yawa da gwamnatocin FCT da suka shude suka bullo da shi ya haifar da bunkasar gidaje masu wayo a babban birnin tarayya (FCT), wanda ya kara habaka harkokin tattara kudaden shiga na cikin gida na gwamnatin babban birnin tarayya tsawon shekaru.
“Takaddun Mallaka na da mahimmanci ga masu mallakar filaye, saboda yana tabbatar da haƙƙin mallaka da bin kaddarorin, tabbatar da amincinta da zamanta, yana taimakawa wajen tabbatar da inshora da kuɗi, haɓaka ƙimar kadarorin da kasuwa, kuma yana ba da kariya ga masu gida da masu haya. ” in ji dan majalisa.
Hon. Soli ya lura cewa masu son haya ko masu siyan irin waɗannan kaddarorin da masu mallakar kadarori a cikin irin waɗannan gidaje na iya ƙarewa cikin yuwuwar rigingimu, batutuwan alhaki, rikice-rikice na shari’a marasa iyaka, da ƙarin haɗari saboda rashin Takardun Shaida.
Da take amincewa da kudirin, majalisar ta umurci kwamitin da ke kan babban birnin tarayya Abuja ya bayar da rahotonsa cikin makonni shida domin ci gaba da aiwatar da dokar.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply