Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa reshen Jihar Bayelsa a Kudancin Najeriya ta tabbatar da cewa wani jirgin ruwa dauke da jami’an zabe zuwa yankin rajista-17 (Koluama) a karamar hukumar Southem Ijaw ta jihar Bayelsa ya kife.
Jami’in wayar da kan Jama’a Wilfred Ifogah, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ba a yi asarar rayuka ba, domin an ceto dukkan jami’an zaben da adadinsu ya kai 12 da ma’aikacin jirgin ruwa.
Misis Ifogah ta ce “Mun yi asarar takardun sakamakon zabe, Naurar cajin waya da jakunkuna masu dauke da kayan sawar ma’aikata”.
Sai dai hukumar ta baiwa masu ruwa da tsaki tabbacin cewa za a sauya duk wasu kayayyakin da suka bata nan da dan wani lokaci domin gudanar da zabe a kananan hukumomin da abin ya shafa.
“Jimillar wadanda suka yi rajista a yankunan da abin ya shafa sun kai 5368 sannan adadin PVC da aka tattara ya kai 5311. INEC na kokarin ganin an gudanar da zabe a yankin da abin ya shafa”.
Sata
Willfred Ifogah ya lura cewa SPO na INEC da aka sanya wa yankin rajista-06 (Ossioma) a karamar hukumar Sagbama an sace shi ne a lokacin da yake jiran ya hau jirgi a gabar kogin Amassoma .
Ta ce an sanar da hukumomin tsaro.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply