Take a fresh look at your lifestyle.

Guinea-Bissau Mai Shekaru 50: Shugaba Tinubu Ya Shiga Bikin Cikar Shekaru

0 87

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya isa kasar Guinea-Bissau domin halartar bikin cikar kasar shekaru 50 da samun ‘yancin kai da kuma ranar sojoji.

 

A cewar sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, shugaban na Najeriya zai hadu a ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, 2023, tare da sauran shuwagabannin gwamnatoci a Bisssu domin bikin, wanda shugaba Umaro Sissoco Embalo zai shirya.

Guinea-Bissau ta yi bikin cika shekaru 50 da samun ‘yancin kai a ranar 24 ga Satumba, 2023, amma gwamnati ta sake tsara dukkan bukukuwan ranar 16 ga Nuwamba, 2023.

 

Ana sa ran shugaba Tinubu zai dawo Najeriya ranar Alhamis.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *