Tsohon Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Bodinga, Dange-Shuni, Tureta, Hon Dr Balarabe Shehu Kakale kana wanda ya dauki dauyin gabatar da kudirin kafa hukumar ingantawa tare da bada ‘yanci ga daliban Makarantun Allo, ko Tsangaya da Almajirci a Nigeria, ya yabawa kokarin gwannatin tarayyar Najeriya karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan yinkurin fitar da tsarin ciyar da daliban Almajirai da na makaratun Allo da Tsangaya a Nigeria.
A cewarsa, wannan ba karamar nasara bace ga shirin na sake inganta karatun allo a Najeriya, ya Kara da cewa wannan fannin ilimi ne mai daraja, inda ya nuna takaicinsa dangane da yadda wasu ke masa rikon ko in kula.
Tsohon Danmajalisar wakilan Najeriya ya Kara da cewa matukar aka yi amfani da wannan dama wajen farfado da farnin da aka durkusar da shi shekaru masu yawa saboda wasu dalilai, za a sami ci gaba mai dorewa.
Ya kuma ce ciyar da wadannan yara masu hazaka da kaifin kwakwalwa, zai kawar da barace barace da wasu ke yi, rashin fahimta da kallon hadarin kaji da ake yi wa wannan shashe na ilimi a Nigeria.
Kana ya yabawa majalisar tarayya to 10, wato (Tenth Assembly) a turance, karkashin jagorancin Rt Hon Tajudeen Abbas na kafa kwamiti na musamman kan kula tare da inganta ilmi Almajirai da Tsangaya da sauran ilimin da ba na Boko ba a Nigeria- wato *House Standing Committee on Alternate Education*.
Wannan sabon babban kwamitin ya samu jagorancin Hon Arch Almustapha Ibrahim Rabah wanda tun tuni sun soma aiki gadan gadan.
Daga karshe Hon Kakale ya yi kira ga gwamnonin Nigeria musamman na yankin Arewacin Kasar Mai jihohi 19 domin suma su aiwatar da wannan shirin da sauran shirye-shiryen gyara da inganta ilimin Tsangaya da Makaratun Allo da gaggawa a jihohinsu domin kare hakkin yara, al’umma da kuma ci gaban kasa gaba daya.
Ak