Take a fresh look at your lifestyle.

GWAMNA ZULUM NA JIHAR BARNO YA KADDAMAR DA TALLAFI GA MATASA

TIJJANI USMAN BELLO

0 322

Gwamnan jihar Barno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da shirin rabawa Matasa Dubu Daya Naira Miliyan Dari da nufin tallafa masu da jari domin dogara da kansu.

 

 

A lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron kaddamar da shirin ga matasan a babban filin Cinema ta Kadafur dake garin Biu.

 

 

Gwamna Zulum, yace” A bisa la’akari da yawaitar Matasa marasa aikinyi gami da talaucin da ya yi katutu a tsakanin alumma dolene mu yi kokarin shawo kan wannan matsalar ta yadda tattalin arzikin jihar zai farfado;

 

“don haka muka yanke shawarar baiwa wadannan Matasan da yawansu ya kai har dubu daya, tallafin kudi Naira miliyan dari daya, ta yadda ko wani mutun zai samu Naira dubu dari daya, musamman ga matasan da suke da bukatar rungumar sana’o’i ko kasuwanci don dogaro da kai”

 

Ga mutane da dama dake gudanar da sana’o’i ko kasuwanci, gwamnan ya ce zai taimaka masu wajen inganta harkokin kasuwanci don habaka tattalin arzikin jihar da ma Kasa baki daya.

 

Gwamna Zulum, har ila yau ya bude babban Makarantar Sakandare ta Islamiyya mai daukan dalibai 1500, ta (Higher Islamic School Biu) wanda alumman garin Biu suka gina, in da ya mika masu Cekin kudi har na Naira miliyan 40, da nufin biyan albashin Malaman Makarantar;

 

kana sai gwamnan ya tabbatar wa daliban cewar da wannan takardar Makarantar ta sakandaren islamiyya zasu iya samun damar karatun dipuloma a manyan makarantun gaba da sakandare, ganin cewar ana koyar masu da darussan turanci da lissafi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.