Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya amince da biyan albashin ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho a matsayin wani mataki na dakile illar cire tallafin man fetur.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Olawale Rasheed ya sanyawa hannu, Adeleke ya ce matakin na daya daga cikin jajircewar sa na kyautata jin dadin ma’aikata da kuma cika alkawarin da ya dauka na daukar matakan jin kai a hankali domin dakile tasirin cire tallafin.
Amincewar wanda ke kunshe a cikin wata takardar da ma’aikatar kula da ma’aikata da inganta karfin aiki ta bayyana cewa ma’aikata za su samu kyautar albashin N15,000 yayin da ‘yan fansho za su karbi N10,000.
Takardar da ke dauke da sa hannun babban sakatare a ma’aikatar Sunday Olugbenga Fadele ta bayyana cewa za a fara bayar da albashin ma’aikata na tsawon watanni shida daga watan Disamba.
“A ranar farko ta shekara ta biyu a ofis, na kaddamar da wannan kyautar albashi tare da sake tabbatar da ajandarmu mai guda biyar wadda ta kunshi jin dadin ma’aikata a matsayin abu na daya,” inji shi.
Sanarwar ta ce an amince da biyan albashin ne biyo bayan tattaunawa da mu’amala da kungiyar kwadago a jihar Osun, ciki har da wakilan kungiyar ‘yan fansho ta Najeriya.
Leave a Reply