Gwamnatin Jihar Kwara dake arewa ta tsakiya a Najeriya a kokarinta na ganin ta kawar da jihar daga dukkan wata barazana da munanan dabi’u, ta bayyana barace-barace da yawo a tituna da masu fama da tabin hankali ke yi a matsayin abin Allah wadai da ban tsoro.
Kwamishinan Cigaban Jama’a, Opeyemi Oluwakemi Afolashade ta bayyana hakan a lokacin da ma’aikatar ta kammala aikin kwashe mutanen a babban birnin jihar.
Afolashade ya koka da yadda ake fama da barace-barace a kan tituna da ake yi wa kallon wata sana’a ce ta kasuwanci a tsakanin wasu mutane, duk da tattaunawa da wayar da kan jama’a da dama da gwamnati ke yi ga masu fama da nakasa da kuma masu rauni a jihar.
Kwamishinan ta jaddada cewa, “ayyukan da aka yi na kwashe mutanen wani bangare ne na ayyukan da ma’aikatar ta rataya a wuyansu da kuma hanyar da za ta kara tabbatar da cewa an tsaftace al’umma daga duk wani nau’i na barazana ga al’umma, ta yadda za a inganta tsaftar muhalli da dabi’u ga jihar,” in ji Kwamishinan.
Ta kuma bayyana cewa jihar Kwara ba za ta amince da barace-barace a kan tituna ba saboda ya saba wa dokar jihar; yana nuna kasala, yayin da yawo na masu tabin hankali shima yana haifar da hatsari ga al’umma.
Afolashade, a yayin atisayen ta nanata cewa za a ci gaba da gudanar da wannan aiki, inda ta kara da cewa ma’aikatar ba za ta kara daukar matakin da ya dace ba, yana mai gargadin duk wadanda ke da hannu da su daina ko kuma su kasance a shirye su fuskanci fushin doka.
A yayin atisayen dai an samu turjiya da kai farmaki kan jami’an ma’aikatar, amma jami’an tsaron farin kaya sun kasance a kasa domin dawo da zaman lafiya.
Don haka Kwamishinan ya yaba da kwazon da jami’an suka nuna a lokacin atisayen yayin da yake neman ci gaba da tallafa wa rundunar a ayyukan da suka biyo baya.
Tawagar ta sun zagaya da ofishin gidan waya/Taiwo-Isale, garejin Tipper, Challenge/Unity Road da Challenge/GRA na babban birnin jihar tare da kwashe mutane masu tabin hankali da mabarata akalla 88 da aka kai daya daga cikin gidajen farfado da ma’aikatar magani, tuhuma da yiwuwar komawa gida.
Leave a Reply